Ana yi wa tubabbun ƴan ta’adda 789 gyaran hali, inji Babban Hafsan Tsaron Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Aƙalla sama da ƴan ta’adda 120,000 ne suka miƙa wuya tare da iyalansu tun da aka ƙaddamar da Cibiyar Atisayen ‘Operation Safe Corridor’ a shekarar 2016, inji Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa.

Ya ce, a halin yanzu cibiyar tana da tubabbun ƴan ta’adda guda 789 da ke ɗaukar horo akan gyaran hali a ƙarƙashin shirin, waɗanda ana tsammanin a yaye su a wannan shekarar.

Janar Musa, wanda Babban jami’in Tsare-tsare da Shirye-shirye na Hedikwatar Tsaro, AVM Sayi Olatunde ya wakilce shi a zaman masu-ruwa-da-tsaki, ya ce suna aiki tuƙuru wajen ganin an miƙa su ga hukumomin ƙasashe da jihohinsu.

Babban Hafsan ya ƙara da cewa, an samar da Operation Safe Corridor ne ganin yadda ake samun yawaitar masu tuba daga ƴan ta’addar ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP.

Ya kuma ce, sun shirya zaman ne musamman don gudanar da miƙa tsofaffin ƴan ta’addar cikin tsari, ya na mai cewa yayin da aka yaye su, za a ba su waɗansu ababe da za su taimaka masu wajen dogaro da kawunansu la’akari da sana’o’in da aka koya masu.

A nasa jawabin, Kodinetan Operation Safe Corridor, Janar Yusu Ali ya ce tun da aka samar da shirin a shekarar 2016, sun yi nasarar yaye mutane 2,190, waɗanda daga ciki, 2,163 ƴan Nijeriya ne yayin da 27 kuma ƴan Kamaru da Chadi da Nijar ne.

By Babaji