
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Talata ne Hukumar yaƙi da Safarar Ɗan-adam, NAPTIP, ta ce ta kama wata tawagar ƴan mata 13 da ake zargin safarar su za a yi zuwa Baghdad, babban birnin ƙasar Iraƙi don harkar karuwanci da wasu ƙasƙantattun ayyuka.
Ta ce, ta yi nasarar hakan ne da haɗin-gwiwar jami’an takwarorinta inda ta gano cewa ƴan matan, waɗanda suke da shekaru 19 zuwa 39, an yaudare su ne da sunan cewa za a sama masu aiki daga wasu jami’an bogi da ake zargin suna gudanar da harkokinsu ne a tsakanin Nijeriya da ƙasashen Gabas ta Tsakiya.
An kama tawagar ne a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja, gabannin ficewa zuwa Iraƙi.
Haka kuma, jami’an hukumar sun ce sun rufe wani shahararren Otel mai suna Three Star a Kwali dake ƙaramar hukumar Kwali a Abuja, inda suka ceto wasu yara mata 11 waɗanda ake zargin ana amfani da su ne a harkar karuwanci.
