
Daga BELLO A. BABAJI
Mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu huɗu suka samu raunuka a lokacin da wani gini ya rushe a wata makarantar kwalejin mata ta GGTC Potiskum dake Jihar Yobe.
Tuni aka garzaya da sauran mutane huɗun da suka jikkata zuwa asibiti don ba su kulawa.
Blueprint ta ruwaito cewa, lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 12 na rana a lokacin da ake tsaka da ɗaukar darussa a wani sashi na ginin ɗakunan karatu guda biyu na ƴan aji biyu a babbar sekandire, wato SS2.

Kowane ɗaya daga cikin ajujuwan na ɗaukar ɗalibai 25 inda a lokacin da abin ya faru kimanin ɗalibai 50 ne aciki.
Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sekandire ta jihar, Bukar Aji Bukar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce sun halarci wajen don ganin halin da ake ciki.
Ya kuma ce, sun ziyarci asibitin da aka kai masu raunukan don duba sauran waɗanda aka kwantar da su, waɗanda ake sa ran sallamar su acikin kwana ɗaya.
Ya ƙara da cewa, sun nemi Ministan Gine-ginen da ya gudanar da bincike game da al’amarin, ya na mai fatan kada irin hakan ya sake faruwa a nan gaba.

