
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta jaddada aniyarta ta ƙoƙarin haɗa kai da ta Tarayya wajen ganin ta kawo ƙarshen cutar poliyo a jihar.
Ta ce a shirye ta ke ta haɗa kai da kuma Gidauniyar ‘Gates Foundation’ da Gidauniyar Ɗangote don toshe giɓin da ake samu a yayin yaƙi da ita.
A wata takarda da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, Gwamna Abba ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da Ministan Lafiya da Ci-gaban Al’umma da wasu wakilan gidauniya biyun a wata kira ta musamman a Fadar gwamnatin jihar.
Ya ce, yana da muhimmanci a haɗa kai da ɓangarorin a ƙoƙarinsa na inganta rayuka da lafiyar al’ummar jihar.
Gwamna Abba ya ce yayin da suke bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu, akwai buƙatar a fuskanci matsalolin da ke damun ɓangaren kiwon lafiya musamman kan batun cutar poliyo da mutuwar jarirai da mata a yayin haihuwa.
Ya sha alwashin samar da shirye-shirye na riga-kafi da na inganta ma’aikatan lafiya da bunƙasa hanyoyin raba kayan aiki don cimma kyawawan manufofinsu.
A nasa jawabin, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya jinjina wa gwamnatin jihar bisa hoɓɓasa da ta yi a ɓangaren, ya na mai cewa za su ba ta cikakken haɗin kai da taimakon da take buƙata wajen cimma nasara.
