NAHCON ta jaddada aniyarta ta kula da mahajjata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), ta haɗa kai da hukumar Saudiyya ta Mashariq al Dhahabia la’akari da rahotanni da ke cewa ta karya ƙa’idar kwangila.

Babban jami’in yaɗa labaranta, Muhammad Ahmad Musa ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce NAHCON ta na iya bakin ƙoƙarinta na Ganin ta kiyaye sharuɗɗan kwangiloli don tabbatar da gaskiya da adalci.

A watan Junairu ne NAHCON da Mashariq al Dhahabia suka ƙulla yarjejeniyar samar wa mahajjatan Nijeriya walwala ta musamman a yayin gudanar da aikin hajjinsu a ƙasa mai tsarki.

A ƴan kwanakin nan ne aka samu wasu rahotonni da ke bayyana cewa hukumar ta Saudiyya ta shirya ɗaukar matakin doka akan NAHCON bisa saɓa wa ƙa’idojin yarjejeniyar.

Saidai, sanarwar ta musanta batun da cewa babu wani yunƙuri mai kama da haka, tana mai cewa aiki ta ke yi tuƙuru wajen ganin mahajjatanta sun samu walwala da kulawa mai inganci gami da rangwamen farashi.

Ya ƙara da cewa, NAHCON za ta cigaba da ƙoƙarin inganta yanayi mai kyau ga walwalar mahajjatan da kuma tabbatar da gaskiya da adalci.

By Babaji