Cutar Nimoniya: Ba lallai na yi rai ba a wannan karon, inji Pafaroma

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Pope Francis, wanda aka fi sani da Pafaroma ya ƙyanƙyasa wa abokan sirrinsa cewa ba lallai ba ne ya tsira daga cutar nimoniya a halin da ake ciki.

A makon da ya gabata ne aka kwantar da babban jagoran kiristocin a asibiti, bayan da likitoci suka ce masa akwai yiwuwar ya rasa ransa matuƙar ya cigaba da zama a Fadarsa ta Vatican.

Gabannin lokacin ne Pafaroma ya yi ta samun kiraye-kiyare na ya fice daga Vatican na wasu ƴan kwanaki.

Bayan haka ne aka garzaya da shi asibitin Gemelli dake Birnin Rome a sakamakon zafin ƙirji da ke damun sa.

Likitoci a asibitin sun duba lafiyarsa ne game da cutar sanyi ta ɓangaren numfashi, wanda hakan ya yi sanadin suka hana shi gudanar da wasu al’amuran yau da kullum.

A ranar Talata ne Vatican a wata sanarwa ta tabbatar da cewa, gwaje-gwaje da aka yi a na’ura da wasu nau’ukan sun nuna cewa Pafaroma na cikin mawuyacin hali.

Sanarwar ta kuma shekaru da dama da suka gabata ne aka cire wani sashi na ƙodar jagoran, wanda hakan ya sa ake ganin ba lallai ya kai labari ba a wannan karon.

By Babaji