Daga USMAN KAROFI
A ranar Alhamis, wata taƙaddama ta kunno kai a majalisar dattawa yayin da shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya umarci jami’an tsaro su fitar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga zauren majalisar. Rikicin ya samo asali ne bayan rahoton da babban mai tsaron majalisar, Mohammed Monguno, ya gabatar, inda ya bayyana cewa Sanata Natasha ta ƙi komawa sabuwar kujerar da aka ware mata. An bayyana cewa wannan sauyi ya biyo bayan ficewar wasu ‘yan majalisa biyu daga jam’iyyar adawa zuwa APC mai mulki.
Duk da umarnin Shugaban Majalisar, Sanata Natasha ta dage cewa an tauye hakkinta, tana mai jaddada cewa tana da damar yin magana daga kujerarta ta baya domin ba ta tsoron Akpabio. Sai dai Akpabio ya yi fatali da buƙatar ta, yana mai cewa ‘yan majalisa ba za su iya magana ba sai daga kujerar da aka ba su. Hakan ya haifar da saɓani, inda Sanata Natasha ta zargi Akpabio da yunƙurin hana ta damar gudanar da aikinta da kuma tozarta ta. Ta ce an sha hana ƙudirorinta kaiwa matakin karatu na biyu a zauren majalisar.
Daga bisani, Sanatoci daga Jihar Kogi sun shiga tsakani domin kwantar da tarzomar, inda Shugaban Sanatocin Jihar, Isa Jibrin, ya nemi afuwar majalisa kan halayyar Natasha. Sai dai wasu sanatoci sun nuna goyon bayansu ga Natasha, inda suka hana jami’an tsaro tilasta fitar da ita daga majalisar. Bayan ɗaukar lokaci ana taƙaddama, Sanata Natasha ta dakatar da ƙorafinta, lamarin da ya ba da damar cigaba da zaman majalisar cikin lumana.
