Turji ya ɓulla Sakkwato, ya ɗora harajin miliyan 25 ga ƙauyuka

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Shahararren jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji, ya sake bayyana a yankin gabashin Jihar Sakkwato, inda ya ƙaƙaba harajin Naira miliyan 25 kan wasu ƙauyuka, kamar yadda ɗan majalisar dokokin jihar, Aminu Boza, ya bayyana. Boza, wanda ke wakiltar mazabar Sabon Birni Gobir, ya ce Turji yana cikin yankunan Isa da Sabon Birni, yana barazanar ƙara tada zaune tsaye a yankin. Ya buƙaci hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki don daƙile wannan barazana.

A yayin wata hira da kafar yaɗa labarai, Shugaban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa Turji yana shirin miƙa wuya bayan da hare-haren sojoji suka raunata ƙarfinsa.
Ya bayyana cewa an hallaka mataimakinsa na kusa da wasu manyan kwamandojinsa, wanda hakan ya tilasta masa sakin wasu daga cikin mutanensa. Duk da haka, Janar Musa ya jaddada cewa Turji ba zai tsira daga fuskantar hukunci ba, domin waɗanda suka aikata kisan gilla ba za su samu mafaka ba.

Sakamakon bayyanar Turji a Sakkwato, tsoro ya sake shigewa mazauna yankin da ke fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga. Masana tsaro sun buƙaci a ƙara haɗa kai wajen kawar da barazanar ta hanyar ɗaukar matakin soja da kuma tsaurara matakan kariya a yankunan da abin ya shafa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yaƙi da ‘yan bindiga a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya.

By ukarofi