Libya ta dawo da mata ‘yan Nijeriya 48 da yara biyu

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar yaƙi da shige da fice ta haram a ƙasar Libya ta kori mata ‘yan Najeriya 48 tare da yara guda biyu daga ƙasar, tare da haɗin gwiwar ofishin jakadancin Najeriya da kuma tallafin hukumar kula da hijira ta duniya (IOM).

An gudanar da wannan atisayen mayar da su gida ta filin jirgin saman Mitiga, domin tabbatar da komowarsu cikin ƙoshin lafiya. Wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin rage wahalhalu ga ‘yan Najeriya da ke fuskantar matsaloli a ƙasashen waje, musamman a wuraren da ake fama da rikici kamar Libya.

Hukumar Migrant Rescue Watch ce ta sanar da hakan a shafinta na X (tsohuwar Twitter) a ranar Laraba, inda ta bayyana cewa mata 48 da yara 2 ‘yan Najeriya sun koma gida ƙarƙashin kulawar ofishin jakadancin Najeriya da IOM.

By ukarofi