
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga waɗanda aka yaye daga Cibiyar Nazarin Manufofi ta Ƙasa (NIPSS) da wasu masu tsara manufa a Nijeriya da su jagoranci aikin kawo sauyi a fasahar zamani da ci-gaban tattali a zamanance.
Ya ce, daga cikin shirye-shiryen gwamnatinsa akwai bunƙasa ayyukan NIPSS da kayayyakin zamani don tabbatar da samun ilimi cikin inganci a Nijeriya.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, a lokacin bikin yaye manyan ɗaliban NIPSS zango na 46 a Kuru dake Jihar Filato.
Shugaba Tinubu, wanda Mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilce shi a taron, ya ce bincike kan tsare-tsare da inganta matasa da amfani da fasahar zamani abubuwa ne da ke da muhimmanci ga samar da gobe mai kyau ga Nijeriya.

Ya kuma yi alƙawarin cewa, shirye-shirye da suka haɗa da faɗaɗa samar da ababan more rayuwa da amfani da fasahar zamani wajen ciyar da tattalin arziƙin ƙasa gaba, za su taimaka wa ƙasar wajen sarrafa baiwa da matasanta suke da ita.
Shugaban ƙasar ya kuma ƙudiri aniyar haɓaka ayyukan NIPSS ta hanyar samar da ɗakin karatu da kayan karatu na zamani don sauƙaƙe hanyoyin samun ilimi ga al’ummar Nijeriya.

