Hukumar tattara haraji za ta sanya tarar N500,000 ga waɗanda ba sa son biya a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji ta Birnin Tarayya, FCT-FIRS, ta yi barazanar tilasta wa waɗanda basa son biyan haraji tarar N500,000 a Abuja.

Shugaban riƙon ƙwarya na hukumar, Michael Ango ya bayyana gargaɗin a ranar Alhamis a Abuja, a lokacin gangamin wayar kan al’umma game da biyan haraji da aka saba yi duk shekara.

Ya ce, duk waɗanda ba su biya harajin 2024 ba zuwa Junairun 2025, za a sanya masu tarar N500,000 a matsayin horo.

Ango ya ce, a lokacin da suka sanya wa’adin 31 ga watan Junairu, 2025, an samu kamfanoni da dama da suka biya nasu, yayin da wasu kuma suka gaza biya, ya na mai jinjina wa na farkon game da ƙoƙarinsu na kiyaye dokar.

Ya kuma ce, lallai za su ɗauki matakin doka akan waɗanda ba su kiyaye umarnin hukumar ba.

Ya ƙara da cewa, za a sake sanya wani wa’adin acikin kwana 30 ga ma’aikata da waɗanda ba su ba na su shigar da bayanan harajin da za su riƙa biya a kowacce shekara.

Dokar ƙasa ta wajabta wa kowane mutum biyan haraji har zuwa ranar 31 ga watan Maris na kowacce shekara, wanda rashin kiyayewa ka iya sa ta zartar da hukuncin akan mutum.

By Babaji