Haɗa hannu da ƴan jarida ƙashin bayan tsaron ƙasa ne, inji Janar Wahab

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Darakta-Janar na Cibiyar Bincike ta Sojojin Nijeriya, (NARC) Manjo-Janar Garba Wahab ya ce haɗa hannu tsakanin sojoji da gidajen jaridu ɗaya ne daga cikin ginshiƙan samar da tsaro a ƙasa.

Daraktan ya bayyana hakan ne a yayin zama da mambobin Ƙungiyar Wakilan Hedikwatar Tsaro (DECAN) a Abuja.

Janar Wahab ya ce, lallai sai ƴan jarida sun riƙa ruwaito rahotannin ayyukan sojoji a tsarin da ba zai haifar da tsaiko ga tsaron ƙasa ko nuna gazawar jami’ai ba.

A cewarsa, gidajen jaridun Turai ba sa ruwaito labaran da ke raina ayyukan sojojinsu, ya na mai kira ga na Nijeriya da su ƙaurace wa irin waɗanda suke da munanan tasiri ga jami’an soji.

Ya ƙara da cewa, matakin rashin yarda da ke tsakanin ɓangarori biyun ya zama wajibi a magance su matuƙar za a yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa.

By Babaji