Yanzu-yanzu: Tsohon Shugaban NYSC, Janar Tsiga ya samu ƴanci kwanaki 22 bayan garkuwa da shi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne tsohon Shugaban Hukumar Kula da Ɗalibai Masu yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ya samu ƴanci bayan shafe kwanaki 22 a hannun waɗanda suka yi garkuwa da shi.

Wani shaida ya bayyana wa manema labarai cewa, a jiya Juma’a ne aka sako Janar Tsiga, wanda a halin yanzu yana karɓar kulawa a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba saboda dalilai na tsaro.

Ƴan bindigar da suka yi garkuwa da shi ƙarƙashin jagorancin Babaro, sun nemi a biya miliyan N250 ne a matsayin kuɗin fansa. Amma ba a san ko an biya wani kuɗi ba kafin sako shi.

Kawo yanzu jami’an gwamnati da hukumomin tsaro da ƴan sandan Katsina ba su ce komai ba game da batun.

A ranar 6 ga watan Fabrairu ne aka yi garkuwa da Janar Tsiga, a gidansa da ke ƙauyen Tsiga, a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina.

By Babaji