Kotu ta tura Ahmad Pasali gidan kaso

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Kamar yadda jaridar mujallar Fim ta rawaito, bayan shigar da ƙara kan ɗan TikTok Ahmed Pasali da ƙungiyar MOPPAN ta yi bisa zargin ƙazafi da ɓata sunan ƴan Kannywood, matashin ya bayyana a gaban kotu a Jos.

Pasali ya musanta zargin, wanda ya sa lauyan shi ya nemi a ba da belinsa.

Alƙali Thomas Nakowa ya bada belin tare da gindaya sharuɗɗan beli, ciki har da ajiyar kuɗi N250,000 da samun wanda zai tsaya masa daga Jos, tare da takardun gidan zama. Amma saboda rashin cika waɗannan sharuɗɗa, an mayar da shi gidan gyaran hali har sai an bi ƙa’idojin.

An ɗage sauraron shari’ar zuwa 5 ga Afrilu. Shugaban MOPPAN na ƙasa, Umaru Maikufi Cashman, ya jaddada cewa ƙungiyar ba za ta lamunci cin mutuncin ƴan Kannywood ba, kuma za su ɗauki mataki kan duk mai yin hakan.

By ukarofi