
Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Zartarwa ta Tarayyar (FEC), ta amince da Naira biliyan 507 da aka ware domin gudanar da aikin sashi na biyu na titin Abuja-Kaduna da Zariya-Kano mai tsawon kilomita 164.
Ministan Ayyuka David Umahi ya bayyana hakan a ranar Litinin, bayan kammala zaman majalisar ƙarƙarshin jagorancin Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban ƙasa dake Abuja.
Ministan ya ce, kuɗin wani ɓangare ne na Naira biliyan 733 da aka ware don ayyukan titina a shiyyoyin Nijeriya.
Haka kuma, FEC ta amince da biliyan N24 na aikin gadar Abakpa a Jihar Enugu wanda ke iyaka da rukuni na 48 na barikin sojoji.
Ya kuma ce, an bai wa CCECC kwangilar aikin ne don rage cinkoson ababen hawa a yankin.
