Zelensky ya amince Amurka ta jagoranci sulhunta su da Rasha – Trump

Spread the love

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky, ya aike masa da wasiƙa inda ya ke sanar da shi aniyar Kyiv, ta ba da goyon baya don cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da Rasha, a ƙarƙashin jagorancin Amurka.

A lokacin da shugaban na Amurka Donald Trump ke gabatar da jawabi a zauren majalisar dokokin ƙasar, ya ce, a wasiƙar da Zelensky ya aike masa, ya ce, Ukraine ta fi kowa buƙatar cimma yarjejeniyar zaman lafiyar.

Wannan dai na zuwa ne sa’oi kaɗan bayan da Amurka, ta sanar da dakatar da bai wa Ukraine duk wani tallafin soji, a yaƙin da ta kwashe sama da shekara uku ta na yi da Rasha.

Haka nan shugaban na Amurka ya ce sun tattauna sosai da Rasha kan rikicin na Ukraine, inda ya ce, ta nuna a shirye take wajen kawo ƙarshen yaƙin.

Tun a watan Faburairun shekarar 2022 ne dai Rasha ta ƙaddamar da farmaki a Ukraine, matakin da masana suka ce ya saɓa wa dokokin Majalisar ɗinkin Duniya, don haka Trump ya ce lokaci ya yi da za a kawo ƙarshensa. RFI.

By ukarofi