
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da samar da tallafi ga ƴan Nijeriya da ke yin jinyar cutar ƙoda, waɗanda daga yanzu za su riƙa biyan N12,000 a madadin N50,000.
Tuni aka fara aiwatar da shirin hakan a wasu cibiyoyin kiwon lafiya a shiyyoyi shida na Nijeriya.
Jaridar ‘Intelregion’ ta ruwaito cibiyoyi da asibitocin da suka fara aiwatarwa kamar haka;
“…Federal Medical Centre (FMC) Ebute-Metta Lagos, the Federal Medical Centre (FMC) Jabi, Abuja, the University College Hospital (UCH) Ibadan, the Federal Medical Centre (FMC) Owerri, and the University of Maiduguri Teaching Hospital (UMTH) Maiduguri.”
Sauran sun haɗa da; “…Federal Medical Centre (FMC) Abeokuta, Lagos State University Teaching Hospital (LUTH) Lagos, the Federal Medical Centre (FMC) Azare, University of Benin Teaching Hospital (UBTH) Benin, and University of Calabar Teaching (UCTH) Calabar.”
An ƙaddamar da shirin tallafin ne a watan Junairu, a Asibitin Koyarwa na Tafawa Ɓalewa dake Bauchi.
Manajar Cibiyar kula da masu cutar ƙoda ta asibitin, Hammatu Haruna ta ce marasa lafiya sun bayyana jin-daɗinsu ga samun tallafin.
Ta ce, a baya biyan asalin kuɗin aikin ya na yi masu wahala, inda a yanzu har sun samu mutane 38 da suka amfana daga tallafin.
Ta ƙara da cewa, Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta samar da duk abinda ake buƙata na ganin shirin ya yi nasara.
