Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bangaren wutar lantarki a Nijeriya na fuskantar matsalar rashin kuɗi, inda kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos) ke gargaɗin yiwuwar rufewa na dogon lokaci.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da GenCos, a wata sabuwar wasiƙa da suka aikewa Hukumar Bayar da Rahoto kan Harkokin Kuɗi ta Nijeriya, FRCN, sun bayyana yiwuwar ƙarin kuɗin lantarki bayan ƙaƙaba sabbin haraji kan kamfanonin wutar lantarki.
Dangane da alƙawuran da aka ɗauka na magance matsalar kuɗi a ɓangaren samar da wutar lantarki, takarda daga Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta biya Naira Biliyan 371 ne kawai ko kashi 19.5 na tallafin Naira Tiriliyan 1.9 da aka samu daga giɓin kuɗin lantarki na bara.
Lamarin ya nuna wani jan-aiki da ke gaban gwamnatocin jihohin da ke karɓar ragamar samar da wutar lantarki daga hukumar NERC.
Rahoton Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) na shekarar 2024 ya nuna cewa GenCos ya biya jimillar Naira Tiriliyan 2.972 na wutar lantarkin da aka samar, amma Naira biliyan 155 ko kashi bakwai cikin 100 na bashin da aka ciyo ne kawai aka alaƙanta da DisCos.
