
Daga BELLO A. BABAJI
A wani sabon al’amari game da rikicin Masarautar Kano, Kotun Ɗaukaka ƙara a Abuja, ta janye hukuncinta na ranar 10 ga watan Junairu, wanda ya amince da gyaran dokar majalisar masarautar Kano da Gwamnatin jihar ta yi, har zuwa lokacin da Kotun Ƙoli za ta yi hukunci.
Kotun Ɗaukaka ƙara a Kano ta jingine umarnin ranar 20 ga watan Yuni da Alƙali Abubakar Liman na Babbar Kotun Tarayya dake Kano ya yi na soke matakan da gwamnatin jihar ta bi na yin kwaskwarima ga dokar majalisar masarautar Kano ta 2024 da kuma naɗa Sarkin Sanusi Lamiɗo Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16.
Kotun Ɗaukaka ƙara dake Kano ta yi zama a Abuja, inda ta ce Alƙali Abubakar Liman ya yi hukuncin ne ba tare da ikon yin hakan ba a dokance.
Kasancewar gwamnatin Kano ba ta gamsu da hukuncin ba, sai ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli da kuma shigar da koken neman Kotun Ɗaukaka ta tsame hannunta acikin shari’ar har zuwa lokacin da ta ƙolin za ta yi hukunci.
A ranar Juma’a ne aka gudanar da shari’ar akan ƙarar da Alhaji Aminu Babba Ɗan.. ya shigar, inda ya nemi kotun da ta haramta wa gwamnatin Kano, Kakakin Majalisar dokokin jihar, Sufeton ƴan sanda, jami’an Civil Defense da sauran jami’an tsaro cigaba da tabbatar da hukuncin Kotun Ɗaukaka ƙara a yayin da aka ɗaukaka ƙara a Kotun Ƙolin.
A yayin hukunci, tawagar alƙalai uku ƙarƙarshin jagorancin Alƙali Abang, ta ce ƙarar ta cancanci shari’a ta yi hukunci akan batun da ta shigar la’akari da sharuɗɗa da ka’idodi da ta cika.
Don haka ne kotun ta umarci ɓangarorin da aka shigar da su ƙarar da su ƙaurace wa tabbatar da hukuncin ranar 10 ga Junairu, wanda ya ƙunshi rushe masarautu har sai Kotun Ƙoli ta yi hukunci.
