
Daga BELLO A. BABAJI
Pafaroma zai koma Fadar Vatican inda zai shafe aƙalla watanni biyu kafin ya murmure, kamar yadda ɗaya daga cikin likitocinsa ya bayyana.
An kwantar da Pafaroma mai shekaru 88 ne a Asibitin Gemelli dake Birnin Rome a ranar 14 ga watan Fabrairu.
Lamarin da ya auku sakamakon rashin lafiyar da ta shafi numfashi wadda ta sauya zuwa nimoniya.
Hakan ya biyo bayan sanarwar da Vatican ta yi ne a makon da ya gabata na cewa jagoran ya na samun sauƙi daga halin da ya shiga.
