An kammala kaso 72 na aikin bututun gas daga Ajakuta zuwa Kano – NNPC

Spread the love

Shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPC), Injiniya Bayo Ojulari ne ya bayyana hakan, inda ya ƙara da cewa aikin gina bututun iskar gas din na (AKK) da ya kai darajar dala biliyan $2.8, na dab da kammaluwa inda yanzu aka cimma kashi 72 cikin 100 na aikin a watanni huɗu na farko na shekarar 2025.

Ci gaban aikin bututun, wani babban tabbaci ne cewa nan ba da jimawa ba, iskar gas mai tsafta ta (CNG) za ta karaɗe Arewacin Najeriya, abinda ka iya janyo karyewar farashin man fetur da kuma ƙarfafa wa masana’antu da sufuri a yankin.

Kazalika aikin wani babban cigaba ne da ke nuna yadda Gwamnatin Tarayya ke jajircewa wajen ciyar da Arewacin Najeriya gaba ta hanyar muhimman ayyukan raya ƙasa.

By ukarofi