‘Yan sanda sun yi bayani kan rahoton mutuwar yarinya a jerin gwanon motocin matar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sanda a Jihar Ondo, ta yi watsi da rahoton bogin da ke cewa wata mota daga cikin jerin gwanon motocin matar Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, ta yi sanadin mutuwar wata ƴar shekara tara a Akure, Babban Birnin jihar, ranar Alhamis.

Kakakin rundunar, DSP Olusola Ayanlade ya ce rahoton na ƙarya ne da aka ƙirƙira don ruɗar da al’umma, wanda aka wallafa daga gidan Sahara Reporters a ranar 17 ga watan Afrilu.

Remi Tinubu ta je Ondo ne da nufin ƙaddamar da shirin kiwon lafiya na ‘Renewed Hope Health Initiative Program’ inda aka raba wa ungozomomi kayan aiki a shiyyar kudu maso yammacin Nijeriya.

Kakakin ya ce, shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa wani direba ne ya buge yarinyar kuma ya tsere da wata mota ƙirar Lexus mara rajista.

Don haka ba ɗaya daga cikin jerin gwanon motocin matar Shugaban ƙasar bane.

Haka kuma, iyayen yarinyar sun ce shekarunta bakwai, saɓanin yadda Sahara Reporters suka ruwaito na cewa tara ne.

By Babaji