Majalisar Wakilai ta dakatar da ganawa da kantoman Ribas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kwamitin kula da lamuran shugaban Jihar Ribas na Majalisar Wakilai ya dakatar da yin zama da Jagoran jihar, VM Ibok-Ete Ibas (mai ritaya).

A ƴan kwanakin nan ne majalisar ta gayyaci Ibas bisa jagorancin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗora masa a jihar bayan sanya dokar ta-ɓaci.

Mai magana da yawun majalisar, Sakin Rotimi ya bayyana hakan a wata takarda.

Ya ce, sun yi haka ne da nufin zaɓar wata ranar don kammala wasu shirye-shirye da ke da alaƙa da zaman tattaunawar.

Majalisar ta ƙafa kwamitin mutane 21 da za su sanya ido kan harkokin shugabancin jihar a ƙarƙashin jagoran.

By Babaji