Filato: Gwamna Mutfwang ya bada umarnin bincikar zargin saka wa shanu guba a Bassa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Jihar Filato, ta bada umarnin gudanar da bincike mai zurfi bisa zargin sanya wa shanu 78 guba a yankin Tafi Gana na Ƙaramar Hukumar Bassa dake jihar.

Kwamishinar Labarai, Hon. Joyce Lohya Ramnap ta ce gwamnatin ta samu rahoton sanya guba ga shanu 36 na wani Mallam Sama’ila Nuhu a ranar 16 ga watan Afrilu a yankin dake Gundumar Zanwar.

Shugaban Miyetti-Allah na yankin, Idris Ya’u ya shaida wa Blueprint a ranar Laraba cewa an sanya guba ga wasu shanu 78 na wani mambansu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar 36 daga cikin su nan take, yayin da aka yanka sauran 42 ganin yadda suka tsinci kansu a mawuyacin hali.

Ya ce, an sanya gubar ne a yalo tare da watsa su a yankunan da ake kiwon dabbobi.

Ya kuma ce, sun sanar da hukumomin tsaro aukuwar lamarin, inda suka yi kira a gare su da kada su ɗauki doka a hannunsu.

Gwamantin jihar ta koka game da lamarin, inda ta umarci Ma’aikatar Ci-gaban Kiwo da ta gaggauta gudanar da bincike a kai.

By Babaji