NAHCON ta ƙaddamar da riga-kafi ga mahajjatan 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), ƙarƙarshin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh ta ƙaddamar da taron riga-kafi ga maniyyata aikin hajjin bana a Abuja, ranar Laraba.

Hakan na ɗaya daga cikin ayyukan da take yi a yayin shirye-shiryen Hajjin shekarar 2025.

Farfesa Saleh ya bayyana ƙoƙarin hukumar wajen ganin ta tabbatar da kula da lafiya da bada kariya ga mahajjatan a yayin da suka yi azamar tafiya ƙasa mai tsarki.

Ya ce, a shirye suke su tabbatar da kula da ka’idodin kiwon lafiya na baki ɗaya mahajjatan, ya na mai kira a gare su da su bada haɗin kai don cimma nasara.

Ya kuma kiraye su da su kiyaye doka da oda a yayin cike ƙa’idodin tafiyar da kuma ƙoƙarin ɗaukar darussan da hukumar ta shirya don ilimantarwa da wayar masu da kai.

By Babaji