Kwankwasiyya Sahlaniyya ta haɗe kan magoya bayan jam’iyyar NNPP a Filato

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI, Jos

A wani ɓangare na ƙoƙarin sake fasalin tafiyar Kwankwasiyya da haɗe kan magoya bayanta a Jihar Filato, tsohon ɗan takarar kujerar Sanata a Shiyyar Filato ta Arewa a zaɓen cike-gurbi na 2024, kuma jigo a jam’iyyar NNPP ta jihar, Honorabul Muhammad Shafi’u Yakubu Sahlan, ya yi kira ga dukkan magoya bayan jam’iyyar NNPP da ɓangarorin mabiya aƙidar Kwankwasiyya su haɗa kansu waje guda, domin dawo da kima da darajar jam’iyyar a wajen jama’ar Filato.

An yi wannan kira ne a yayin wani taron ganawa da shugabannin duka ɓangarorin jam’iyyar da aka gudanar, da nufin sake ƙulla wata sabuwar tafiya mai ƙarfi da za ta haɗe kan kowanne ɓangare, don bunƙasa tasirin jam’iyyar NNPP a Jihar Filato, da kuma jaddada goyon bayansu ga tafiyar madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

An jima ana ta ƙorafi game da rabuwar kai da ɓangarorin Kwankwasiyya da shugabannin NNPP a Jihar Filato ke fuskanta, wanda hakan ya sa kowa da inda ya sa gaba, a dalilin haka tasirin jam’iyyar ya fara mutuwa a zukatan masoya da mambobin jam’iyyar. Sai dai sakamakon jajircewa da ƙoƙarin da wannan ɗan siyasa, Hon. Shafi’u Sahlan yake yi ne ya sa aka ga dacewar sake dawo da kwarjinin jam’iyyar, wacce a zaɓen cike-gurbi na 2024 ta zo a mataki na biyu.

“Ina so mu haɗu a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya, mu farka daga barcin da muke yi, mu haɗa ƙarfin mu waje guda, domin cimma muradun jagoranmu Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na inganta cigaban Nijeriya. Yadda ýaýa da jikoki da za su taso nan gaba za su yi alfahari da gudunmawar da muka bayar.” Cewar Sahlan.

Sauran shugabannin tafiyar Kwankwasiyya a Jihar Filato irin su Hon. Abubakar Sabo First Bank, Muƙaddashin Sakataren Jam’iyyar NNPP a Jihar Filato, da Shugaban Matasan NNPP na jihar, Sudais Salim, da Shugaban reshen NNPP a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, Hon. Sani Aliyu Babanladi, sun bayyana goyon bayansu da wannan yunƙuri na Sahlaniyya, don sake kyautata tafiyar Kwankwasiyya, tare da alƙawarin bashi cikakken goyon baya da haɗin kai.

Sun kuma koka tare da ɗorawa kansu laifin wasu kurakurai da aka samu a baya, waɗanda suka jawo wa Jam’iyyar koma-baya a wajen magoya bayanta, tare da sake jaddada aniyarsu ta ƙara dawo da tagomashin madugun Kwankwasiyya a idanun al’ummar Filato da kuma bunƙasa tasirin Jam’iyyar NNPP, don samun ƙarin magoya baya.

Hajiya Aisha Yakubu Adam, wata jigo a tafiyar Kwankwasiyya a matakin ƙasa da Jihar Filato, ta jinjinawa Hon. Shafi’u Sahlan bisa jajircewarsa da kishin da yake nunawa a wannan jam’iyya. Tare da kira ga dukkan ɓangarorin siyasar Kwankwasiyya su bashi goyon baya da haɗin kai, don a cimma nasarar sake gina ƙaƙƙarfar jam’iyya da za ta yi gogayya da kowacce jam’iyyar siyasa a Jihar Filato.

An raba jajayen huluna ga wasu sabbi da tsofaffin magoya bayan Kwankwasiyya, domin sake jaddada aƙida tare da ƙaddamar da shirin sabuwar tafiyar amana da aka yi wa taken, ‘I concur with Kwankwaso for a better Nigeria.’

By ukarofi