Fadar Vatican ta ayyana 26 ga Afrilu a matsayin ranar jana’izar Pafaroma

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jagororin Fadar Vatican sun ce, a ranar Asabar ne za a gudanar da jana’izar Pafaroma, yayin da manyan shugabannin ƙasashen duniya kamar su Donald Trump na Amurka da Volodymr Zelensky na Ukraniya suka ce za su halarta.

Pafaroma, wanda ɗan asalin ƙasar Argentina ne, ya rasu ne yana da shekaru 88 a duniya biyo bayan fama da wani rashin lafiya da ya shafe makonni a kai.

Za a yi jana’izar ne da misalin ƙarfe 10 na safe a Saint Peter’s Basilica dake Fadar ta Vatican a birnin Rome na ƙasar Italiya.

Tuni dai Gwamnatin ƙasar ta sanar da hutun kwanakin biyar ga ma’aikata na jimamin mutuwar shugaban Kiristocin, wanda ya shafe shekaru 12 a muƙamin.

Za kuma a binne shi ne a maƙabartar Basilica of Santa Maria Maggiore, wadda ke da nisa wani adadi na kilomita daga Vatican, kamar yadda ya bada wasiyya.

By Babaji