Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban hukumar gudanarwa na hukumar bada agajin gaggawa SEMA kuma mataimakin gwamnan Jihar Katsina Farouk Lawal Joɓe ya sanar da haka a wajen bikin bada tallafi a ofishin hukumar SEMA.
Ya ce wannan shine karo na 90 da gwamnatin Dikko Raɗɗa ke bada irin wannan tallafi ga waɗanda iftala’in gobara da sauran bala’o’i ya shafa a jihar.
Farouk joɓe ya bayyana cewa a kwanan baya gwamnatin Jihar ta raba tallafi na kuɗi Naira miliyan 450 ga mutane fiye da 1000 da iftala’in ambaliyar ruwan sama ya shafa.
Ya ce wannan tallafi ba wai matsayin diyya gwamnati ta biya ba, taimakawa ne ga waɗanda iftala’in ya shafa su rage raɗaɗin asarar da sukayi.
Haka kuma mataimakin gwamnan yayi magana akan harkar tsaro a jihar da yace a yanzu zaman lafiya ya fara samuwa a jihar.
Sai yayi kira ga al’ummar jihar da su cigaba da yiwa gwamnatin jihar addu’a tare da bada goyon baya wajan ƙoƙarin da take na kawo zaman lafiya a jihar da cigaban al’umma.
A nata jawabin, babban darakta na hukumar SEMA a jihar Hajiya Binta Husaini Dangani ta yi godiya ga gwamnatin Dikko Raɗɗa kan goyon bayan da yake bai wa hukumar wajen aiwatar da aikace-aikacen ta.
Sai tayi kira ga gwamnatin jihar da ta taimakawa hukumar a wajen gudanar da hidimar da ta sa a gaba.
Sun kuwa haɗa da horas da jami’an hukumar da tanajin kayan abinci domin tunkarar damina mai zuwa.
Mutanen da su kayi jawabi a wajen bikin sun haɗa da babban jojin jihar mai shari’a Musa Ɗanladi Abubakar da wakilin Sarkin Katsina.
