An ga giftawar Kwankwaso a Villa

Spread the love

*Raɗe-raɗin komawar Kwankwaso APC ya ƙaru

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Maganganu suna ta yawo kan batun cewa, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zai koma Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, musamman a wayewar garin ranar Alhamis bayan da wasu majiyoyi suka shaida cewa, an ga giftawarsa a Fadar Shugaban ƙasa.

“Mu na shirin fita daga Fadar Shugaban ƙasa, sai aka ce mana, ‘ga Kwankwaso can ya shigo zai gana da Maigida’” inji wata majiya mai tushe, wacce ta nemi Blueprint Manhaja ta sakaya sunanta.

Masu maganganu dai suna cewa, tsohon gwamnan na Kano zai fice daga jam’iyyarsa ta NNPP, wacce ya yi takarar shugaban ƙasa a cikinta a zaɓen 2023. Sai dai, Kwankwaso bai fito ya ce wani abu ba kan raɗe-raɗin cewa zai koma tsohuwar jam’iyyarsa ta APC. Amma dai makusantansa da manyan jiga-jiga a cikin jam’iyyar NNPP sun fito sun musanta wannan jita-jitar da ake yaɗawa. 

Amma akwai wasu muhimman abubuwa da suka faru kan batun komawar Kwankwaso zuwa jam’iyyar APC, inda a cikin makon nan Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa Jam’iyyar NNPP shaguɓen cewa ‘ta mutu murus’, inda ya yi nuni da cewa shi kansa Kwankwason zai koma APC ne.

Ko bayan haka ma, an yi ta raɗe-raɗen cewa, an ga Kwankwaso a Fadar Aso Rock da ke Abuja, domin tattaunawar sirri da Shugaba Tinubu kan batun sauya sheƙar tasa. Wata majiya, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa Blueprint Manhaja cewa, wannan ganawar har zuwa lokacin wallafa rahoton nan ba a fitar da wata sanarwa kan ganawar ba.

Sai dai wata majiya daga cikin Jam’iyyar APC ta bayyana cewa, wannan yunƙuri na tsohon Gwamnan Jihar Kano ya haifar da fargaba a cikin jam’iyyar.

Majiyoyin jam’iyyar sun bayyana wa jaridar Manhaja cewa wannan yunƙuri da ake cewa, ya samo asali ne daga yarjejeniya tsakanin Shugaban ƙasa Bola Tinubu da jagoran na NNPP, ya janyo rashin jin daɗi a ɓangaren Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, da kuma Sanata Barau Jibrin, da ke nuna sha’awar neman tikitin takarar gwamnan Kano a 2027.

Baya ga Kwankwaso, wasu ‘yan majalisar tarayya uku na NNPP sun gana da shugaban jam’iyyar APC ta ƙasa a makon da ya gabata kafin sanar da sauya sheƙarsu zuwa jam’iyyar mai mulki.

Duk da cewa, sakatariyar ƙasa ta NNPP da reshen Kano suna ci gaba da musanta raɗe-raɗin sauya sheƙar Kwankwaso, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa da na jihar Kano sun tabbatar da yunƙurin a maganganunsu cikin makon da ya gabata.

Bincike ya nuna cewa, yayin da Tinubu ke ƙoƙarin samun goyon bayan Kwankwaso da magoya bayansa domin zaɓen 2027 saboda tasirinsa a Kano, wasu jiga-jigan APC na fargabar cewa hidimar da suka yi za ta tashi a tutar babu a yarjejeniyar da Kwankwaso da NNPP.

Wani jigo a jam’iyyar ya shaida wa Blueprint Manhaja cewa, Shugaban APC na Kano yana samun ƙarfin gwiwa daga wasu masu ruwa da tsaki a Abuja da ka iya rasa komai sakamakon kusancin da ake samu tsakanin Shugaba Tinubu da Kwankwaso da ’yan majalisar NNPP.

Majiyar ta ƙara da cewa, an sha alwashin bai wa ’yan majalisar NNPP da suke shirin sauya sheƙa tikiti kai tsaye, domin dawo wa Majalisar Tarayya.

“Idan har Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yanke shawarar bin Kwankwaso, hakan na nufin cewa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, zai yi watsi da burin zama gwamna a 2027,” inji majiyar.

Sai dai a wata hira ta wayar tarho da jaridar Nigerian Tribune, Ladipo Johnson, wanda ya tabbatar da yiwuwar sauya sheƙar Kwankwaso, ya bayyana cewa, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa har yanzu na tuntuɓar masu ruwa da tsaki ne.

Amma duk yunƙurin da Wakilin Blueprint Manhaja ya yi don ji daga Fadar Shugaban ƙasa da ɓangaren Kwankwaso ya ci tura, har zuwa haɗa wannan rahoto.

By ukarofi