Majalisar dokokin Zamfara ta dare gida biyu

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau 

Wani rikicin siyasa ya kunno kai a Jihar Zamfara yayin da Majilisar Dokokin Jihar ta dare biyu, inda wasu ‘yan majalisar suka kafa tasu majilisar daban.

’Yan majalisar dokokin jihar ta Zamfara guda 10 da suke zargin Kakakin majalisar, Rt. Hon. Bilyaminu Ismail Moriki, ya dakatar da su bisa bayyana ƙalubalen tsaro da ’yan mazaɓarsu suke fuskanta ya haifar da kafa wata majalisar dokokin jihar, inda suka bayyana dakatarwar a matsayin “ba bisa ƙa’ida ba”.

’Yan majalisar sun naɗa Hon. Bashar Aliyu Gummi a matsayin shugaban majalisar a lokacin da suka bayyana tsige kakakin majalisar, Hon Bilyaminu Moriki, a farkon shekarar da ta gabata bisa zargin tafka maguɗi da rashin ɗa’a.

A lokacin zama na farko da suka yi a damuwar majalisar dokokin tasu a Gusau, Babban Birnin Jihar ta Zamfara, ranar Laraba, sabon Kakakin ɓangaren Hon. Bashar Aliyu Gummi mai wakiltar mazaɓar Gummi ta 1 bayan tattaunawa da aka kwashe kusan awanni biyu suna yi tattaunawa, ya bayyana cewa ‘yan majalisar sun ba wa gwamna Dauda Lawal wa’adin wata ɗaya inda ya kamata a magance duk wasu matsalolin da suka shafi ayyukan ‘yan ta’adda, garkuwa da mutane da sauran munanan laifuka.

Mambobin da suka fito daga jam’iyyun siyasa APC da PDP sun koka da yadda gwamnatin jihar ta take nuna halin ko in kula akan matsalar tsaro a jihar. 

Sun zargi gwamna Dauda da kashe maƙudan kuɗaɗe kan wasu abubuwa marasa muhimmanci yayin da talauci da rashin tsaro suka mamaye ƙananan hukumomin jihar 14 a daidai lokacin da gwamnatin jihar ta ƙi jajenta wa waɗanda ‘yan ta’adda suka kai wa hari ko kuma sun rasa ‘yan uwansu a hannun a sakamakon hare-haren yan ta’adda a jihar.

Sun bayyana  cewa dakatarwar da aka yi musu ya biyo bayan ƙin yin shiru ne yayin da kashe-kashen da ‘yan bindiga ke ci gaba da yi a jihar. 

‘Yan majalisar sun buƙaci gwamnatin jihar da ta sauya halinta na rashin goyon bayan jami’an tsaro da suke sadaukar da rayuwarsu wajen kare ‘yan ƙasa ta hanyar tabbatar da cewa ya ba su duk wani tallafin da ya dace. 

Hakazalika, ‘yan majalisar da suka nuna bakin cikin su kan rashin goyon bayan da gwamnatin Dauda Lawal ke baiwa jami’an tsaro, sun zargi gwamnati da rashin yi wa jami’an tsaronta kariya (Askarawa), yanayin da yayi sanadiyayar kashe sama da rabin rundunar a arangamar da suka yi da miyagu. 

Sun yi nuni da cewa gwamnan ya yi ta’aziyya ga iyalan jami’an tsaron da aka kashe waɗanda suka rasa rayukansu a bakin aiki tare da bai wa iyalansu aƙalla Naira miliyan 10 ga kowane iyalan da abin ya shafa.

Sun roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta janye matakin da ta ɗauka na korar ma’aikatan gwamnati sama da 4,000 ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba, ganin cewa hakan na da illa ga jihar musamman saboda rashin tsaro da Zamfara ke fama da shi.

‘Yan majalisar sun yi ƙorafin cewa, idan waɗanda ake kira abokan gwamnan, musamman waɗanda suka fito daga jihohin Neja, Kaduna da Adamawa za su iya gina gidaje na biliyoyin Naira da sayen kadarori a jihohinsu jim kaɗan bayan sun ziyarci Jihar,  gwamnan ba shi da wata hujjar rage yawan ma’aikatan jihar bisa  uzuri na rashin isassun kudade shigar jihar. 

Don haka suka ci gaba da cewa, duk waɗanda aka kora a mayar da su bakin aiki tare da ba su albashi da sauran haƙƙoƙinsu a kan kari. 

Mambobin da suka halarci zaman sun haɗa da Hon. Aliyu Ango Kagara, Mamba mai wakiltar Talata Mafara ta Kudu, Hon. Ibrahim Tudu Tukur Bakura, Memba mai wakiltar Bakura, Hon. Nasiru Abdullahi Maru, Memba mai wakiltar Maru ta Arewa. Hon. Faruk Musa Dosara memba mai wakiltar Maradun 1, Hon Bashar Aliyu memba mai wakiltar Gummi 1, Hon Barista Bashir Abubakar Masama memba mai wakiltar Bukkuyum ta Arewa, Hon Amiru Ahmed memba mai wakiltar Tsafe ta Yamma, Hon Basiru Bello mamba mai wakiltar Bungudu ta Yamma sai kuma Hon Mukhtaru Nasiru ɗan majalisar mai wakiltar ƙaura Namoda ta Arewa.

By ukarofi