Gwamnatin mulkin soja a Burkina Faso ta ce, hukumar leƙen asirin ta daƙile wani yunƙurin kifar da gwamnatin mulkin soji a wannan wata na Afrilu. Ta ce an shirya yunkurin juyin mulkin ne a Ivory Coast.
Shugaban riƙon kwarya, Ibrahim Traore ya sha zargin Ivory Coast da hannu a yunƙurin dagula zaman lafiyar ƙasarsa
ya yi iƙirarin cewa, an gano maharan ne a makwabciyar ƙasar Ivory Coast.
Traore, kyaftin ɗin soja wanda shi kansa ya hau karagar mulki a shekara ta 2022 ta sanadiyyar juyin mulki, ya sha zargin Ivory Coast da bai wa abokan hamayyarsa mafaka.
“Ayyukan da hukumar leƙen asiri ta gudanar ya bankaɗo wani babban maƙarƙashiyar da ake shiryawa ƙasarmu wanda babban burinsa shi ne haifar da ruɗani bakiɗaya,” inji ministan tsaro Mahamadou Sana a wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar.
“A bisa shirin ‘yan ta’addan, sun yi yunƙurin kai wa fadar Shugaban ƙasar Burkina Faso hari a ranar Laraba, 16 ga Afrilu, 2025, da wasu gungun sojoji da maƙiya ƙasar suka ɗauka aiki,” inji shi.
Ya ƙara da cewa “Masu kitsa lamarin da ke wajen ƙasar duk suna cikin ƙasar Ivory Coast.”
Ya kuma ambaci wasu tsaffin hafsoshin soja biyu, Manjo Joanny Compaore da Laftanar Abdramane Barry, a matsayin waɗanda suka shirya juyin mulkin da ake zargin sun shirya yi.
A cewar Sana, an yi wa wasu jami’ai goma sha biyu tambayoyi da wasu jami’an da ba na gwamnati ba, ciki har da kwamandan Ouedraogo Frederic.
Tun bayan da gwamnatin mulkin soji ƙarƙashin jagorancin Traore ta karƙi mulki a watan Satumban 2022, ta ke ƙara murƙushe mutanen da take ganin suna adawa da gwamnatinta, tare da yin garkuwa da mutane da kuma kame ba bisa ka’ida ba.
An kama jami’an soji goma sha biyu da suka haɗa da jami’ai biyu a makon da ya gabata bayan da magoya bayan gwamnatin mulkin sojan suka zarge su da shirin “hargitsa” gwamnati, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Litinin. (Premium Times)
