Asusun bada lamuni na duniya, wato IMF ya zaftare hasashen haƙakar tattalin arziƙin Amurka da Chana da wasu ƙasashen da dama, wanda ya ce yana da nasaba da harajin kasuwancin da Washington ke laftawa abokanan hulɗarta mafi ƙololuwa da ka gani cikin shekaru 100.
Asusun na IMF cikin alƙaluman da ya fitar a ranar Talata game da hasashen haƙakar tattalin arziƙin ƙasashe ya ce, durƙushewar ko kuma koma bayan ba zai tsaya kaɗai kan Amurkan da Chana ba, har ma da tarin ƙasashe lura da kasancewar Washington da Beijing jagororin tattalin arziƙi da kuma hada-hadar kasuwanci a duniya.
Alƙaluman na IMF da ke fita kwanaki 10 bayan harajin kasuwancin da Trump ya ƙaƙabawa ƙasashe kodayake ya dakatar da na wasu daga cikinsu, ya nuna cewa hasashen shekarar nan zai samu naƙasu da kashi 0.5 zuwa maki 2.8 daga maki 3 a shekarar da muke ta 2025, yayinda a 2026 tattalin arziƙin zai sake ganin babbar komabaya wanda ke nuna rashin tabbatuwar hasashen samun tagomashin kashi 3 a shekarun na 2025 da 2026.
IMF ya ce tattalin arziƙin duniya bakiɗaya zai yi tafiyar hawainiya fiye da tsammani a watan Janairun baɗi inda shugaban sashen tsare-tsare na IMF Pierre-Olivier Gourinchas ke shaidawa manema labarai cewa duniya na shiga wani sabon babin yamutsin tattalin arziƙi da ke ƙoƙarin rushe tsarin tattalin arziƙin da aka shafe shekaru 80 ana ginawa.
Acewar IMF, matakin laftawa juna harajin daga ƙasashe da kuma rashin tabbas kan makomar tarin manufofin tattalin arziƙin ƙasashe na matsayin kan gaba wajen kassara hada-hadar duniya bakiɗaya. RFI
