Kamar yadda RFI ta ruwaito, Shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahama ya dakatar da shugabar Kotun ƙolin ƙasar, Mai shari’a Gertrude Araba Torkonoo saboda zargin aikata laifuffuka.
Rahotanni sun ce dakatarwar ta biyo bayan takardun ƙorafi guda uku da aka gabatar domin cireta, saboda sauya takardun kotu da kuma amfani da kuɗaɗe ta hanyoyin da ba su kamata ba.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar John Mahama ya ce ɗaukar matakin ya biyo bayan tintibar ƴan majalisar ƙasa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, wanda ya bada damar dakatar da ita har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Ya zuwa yanzu ba ayi cikakken bayani akan ƙorafe-ƙorafen da masu bincikenta guda biyar za su mayar da hankali akai ba.
Sabon shugaban na Ghana Mahama da ya karƙi ragamar mulki a watan Janairu, ya sha alwashin tunkarar matsalar cin hanci da rashawa a ƙasar.
Rahotanni sun ce mai shari’a Gabriel Pwamang daga kotun ƙolin zai jagoranci kwamitin binciken wanda ke ɗauke da babban mai bincike na ƙasa Daniel Domelevo.
An dai naɗa Torkonoo mai shekaru 61 a matsayin shugabar Kotun ƙolin ce a watan Yunin shekarar 2023, kuma ta zama ta 15 cikin jerin waɗanda suka riƙe muƙamin, kana kuma mace ta uku a tarihin ƙasar ta yammacin Afrika.
Yayin da waɗanɗa suka gabace ta suka kammala wa’adin su ko kuma suka fuskanci matsalar siyasa, ita ce ta farko da za a dakatar daga aiki kana kuma a gudanar da bincike akan ta.
