Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A yayin da ake ta cece-kuce a tsakanin ’yan Nijeriya kan amincewar gwamnati na kashe Naira Biliyan 10 wajen samar da lantarki mai amfani da hasken rana na sola a fadar Aso ɓilla da ke Abuja, Fadar Shugaban Nijeriya ta mayar da martani.
Fadar Shugaban ƙasa ta fito fili ta kare matakin bayan ’yan Nijeriya sun matsa lamba ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan lamarin.
Mai magana da yawun Shugaban ƙasa Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya bayyana a shafinsa na ɗ cewa ko a fadar shugaban ƙasar Amurka ana amfani da sola.
Bayo Onanuga ya ce, “Fadar shugaban ƙasar Amurka (White House) na amfani da sola”.
Onanuga ya faɗi haka ne domin nuna cewa amfani da wutar sola a muhimman wuraren gwamnati ba sabon abu ba ne.
Wutar solar da za a samar a Aso Rock za ta ba da wuta mai ɗorewa ga gidan shugaban ƙasa, ofisoshin gudanarwa da kuma wasu muhimman gine-gine.
An bayyana cewa hakan zai ƙara inganta ingancin wutar lantarki da rage dogaro da na’urar janareto, tare da rage kuɗin da gwamnati ke kashewa kan lantarki a tsawon lokaci.
Onanuga ya haɗa da bidiyo na wani aikin samar da sola da aka aiwatar a Fadar White House, inda aka nuna dalilan da suka sa gwamnatin Amurka ta zaɓi amfani da sola a shekarun baya.
Rahoton Solar Reɓiews ya ce, tun a shekarar 1979 lokacin mulkin shugaban ƙasa Jimmy Carter, aka saka allunan wutar sola guda 32 a saman rufin White House don ɗumama ruwa.
Duk da cewa waɗancan allunan ba su daɗe ba bayan mulkin Carter, a shekarar 2017 ya sanya allunan wutar sola kimamin 4,000 a gonarsa da ke Georgia.
A lokacin da ya samar da wutar sola gonar shi, Jimmy Carter ya samar da wutar da ke isar rabin buƙatun mutanen garin Plains.
A yanzu haka dai wasu ‘yan ƙasa na yaba wa ƙoƙarin gwamnati na rungumar wutar sola, yayin da wasu ke bayyana damuwa kan kuɗin da za a kashe wajen aikin.
