Za a kammala aikin jirgin ƙasa Kaduna-Kano a ƙarshen shekara – Ma’aikatar Ayyuka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ana shirin kammala aikin tashar jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano nan da ƙarshen shekarar 2025.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da ma’aikatar sufuri ta fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Gina tashar jirgin kasa mai tsawon kilomita 202 daga Kaduna zuwa Kano, akan kuɗi dala biliyan 1.2, na samun  wani gagarumin ci gaba, inda za a kammala shi nan da ƙarshen 2025.

Tashar jirgin ƙasa ta Kaduna zuwa Kano ta yi daidai da na Legas, wanda ya kai sama da murabba’in mita 13,000, wanda tun farko aka ɗaga masa tuta a matsayin tashar jirgin aasa mafi girma a Nijeriya.

Hakazalika, a cewar sanarwar, tashar jirgin ƙasa ta Zawaciki, za ta kasance cibiyar layin dogo daga Kano zuwa Katsina, kuma ta yi daidai da Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Ya ƙara da cewa, ana sa ran jihar Kano za ta samu tashoshi uku, ɗaya a Yako, Madobi, da Zawaciki.

By ukarofi