Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shahararren ɗan jaridar nan, Ahmed Isah, wanda aka fi sani da Ordinary President kuma mamallakin gidan rediyo da talabijin na Brekete Family, wanda ya yi fice wajen gwagwarmayar ƙwato wa talakawa haƙƙinsu da waɗanda aka zalunta, ya fito ya cire wa ɗumbin jama’a shakku da ruɗanin da suka shiga na jita-jitar cewa yana cikin wani hali, inda wasu suke zargin yana gidan yari, wasu ma suna tunanin an kashe shi.
Ahmed Isah wanda ya kwashe kwana da kwanaki ba a ganinsa kuma ba jin ɗuriyarsa a cikin shirye-shiryen da suke gabatarwa a Brekete Family, wanda ya fi gabatarwa shi da kansa, ya ce yana cikin ƙoshin lafiya, kuma ya gode wa duk waɗanda suka nuna damuwarsu na rashin ganinsa da ba a yi.
Kazalika, ya kuma ƙara jaddada aniyarsa na cigaba da aikin da yake yi na kare haƙƙin al’umma, inda ya ce babu wata baraza da za ta ba shi tsoro ya daina aikin da yake yi.
Ya ƙara nanata cewa, “na san cewa azzaluman ƙasar nan ba sa ƙaunata, kuma ba sa ƙaunar mai ƙaunata, amma abin daɗin masoyana sun fi maƙiyana yawa.
Ahmed Isah ya ce yana fuskantar barazana iri-iri. Sai dai a ƙarshe ya nuna ko da bayan ransa, akwai masu ɗorawa daga inda ya tsaya.
Oridinary President dai yana fuskantar ƙalubale daban-daban daga wajen manyan ƙasar nan, inda ko kwanakin bayan sai dai Majalisar Dattawan Nijeriya ta gayyace shi domin cire mata shakku akan gidan rediyonsa da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya yi iƙirarin bai san da shi ba.
