Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Siminalayi Fubara, dakataccen Gwamnan Jihar Ribas, ya ziyarci Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya, a kwanakin baya a gidansa da ke Abuja, a wani yunƙuri na sasantawa biyo bayan rikicin siyasa da aka shafe watanni ana gwabzawa, wanda ya kai ga kafa dokar ta-ɓaci a jihar mai arzikin man fetur.
Ganawar ta faru ne kwanaki kaɗan bayan ganawar Fubara da Shugaba Bola Tinubu a Landan kan rikicin siyasar.
Idan dai za a iya tunawa, shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas mai arzikin man fetur tare da dakatar da Fubara da wasu zaɓaɓɓun jami’ai na tsawon watanni shida.
Shugaban a yayin ganawar da aka yi a Landan ya umurci Fubara da ya je ya sasanta da shugabanni da ɓangarorin da abin ya shafa a jihar Ribas.
Sai dai Premium Times ta ruwaito cewa Fubara ya bi umarnin ne yayin da ya je gidan Wike a Abuja tare da Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun da Olusegun Osoba, tsohon gwamnan jihar.
“An kawo Fubara gidan minista ne a ranar Juma’a, 18 ga Afrilu. Ya rusuna wa Wike yayin da yake riƙe da ƙafafunsa yana kiransa, ‘My Oga’,” inji ɗaya daga cikin majiyoyin da suka yi magana da jaridar.
Majiyar ta ƙara da cewa, “Ya kasance a gidan Wike har zuwa safiyar Asabar, 19 ga Afrilu.”
Mai magana da yawun Wike, Lere Olayinka, ya tabbatar da cewa taron ya faru, amma ya ce bai da masaniya kan abin da aka tattauna.
