Ranar Ma’aikata: Yadda hauhawar farashi ke dagula rayuwarsu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yayin da duniya ke murnar zagayowar Ranar Ma’aikata a kowace ranar 1 ga watan Mayu, ma’aikatan NIjeriya na cikin wani hali na damuwa da tashin hankali.

An ware wannan ranar ne domin girmama ƙoƙarin ma’aikata a duniya, amma ga ma’aikatan Nujeriya, wannan rana na tuna musu da matsalolin da suke fuskanta a kowace rana.

Waɗannan matsaloli sun haɗa da ƙarancin albashi da wahalar rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi da wahala wajen aiki da kuma rashin ingantattun yanayin aiki da dai sauran su.

Yawanci ma’aikata a Nijeriya suna bayyana takaicinsu dangane da yanayin da suke ciki a ƙasar.

Tuni ma’aikatan gwamnati da aka tura su zuwa gefe suna ɗaukar dabaru daban-daban don rage nauyin sufuri, gami da rabon ranar aiki. Akwai fargabar yanayin na iya ƙara wargaza ayyukan ma’aikatan gwamnati, waɗanda ba su da kayan aiki.

A shekarar 2018, ana sayar da rabin kiret na kwai a kan kusan N494.43.

A yau, kiret ɗin kwai ɗaya ya kai Naira 6,000. Hakan na nufin mafi albashin ƙarancin ma’aikata na N70,000 zai iya sayen kiret ɗin kwai 11 ne kacal yayin da mafi ƙarancin albashi a da N30,000 a kan farashin kiret cin kwai N500 kan iya sayen kiret 60.

A shekarar 2018 kuma, matsakaicin farashin tumatir kilo ɗaya ya kai N271. Haka adadin ya haura N5,000 a yau. Hakan na nufin mutum zai buƙaci ƙarin kuɗin shiga sau 18 a cikin shekaru bakwai da suka gabata don ci gaba da samun walwala iri ɗaya idan aka auna hakan ta hanyar amfani da tumatur kawai. Haka kuna, mafi ƙarancin ma’aikata ya ƙaru da kashi 133 kawai.

Loka guda na shinkafar da aka shigo da ita ya kai Naira 360 a shekarar 2018 a yanzu an kai Naira 1,640 wanda ya haura sama da kashi 500 cikin 100.

Haka kuma, hayar ɗaki ɗaya a cikin garin Legas a duk shekara ya kai kusan 200,000 a shekarar 2018. Matashin ma’aikaci mara aure zai buƙaci ya ƙara kasafin kuɗin sau huɗu zuwa aƙalla N800,000 don biyan gida ɗaya.

By ukarofi