Jami’an tsaron NAYES sun yaba wa G.M Abdullahi Bala kan jagoranci nagari

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Jami’an wani hukumar tsaro na musamman na gwamnatin jihar Nasarawa da ake kira NAYES sun yaba wa sabon shugaban su wato Janar manajan hukumar Abdullahi Bala dangane da tsarinsa na musamman na tabbatar da kyakkyawar tsare-tsare da cikakken kulawar jin daɗinsu a yayin da suke gudanar da ayyukansu na tsaro a faɗin jihar Nasarawa kawo yanzu a cikin shekara guda kaɗai da ya yi a kujerar ta Janar manajan hukumar. 

‘Yan tsaron sun bayyana haka ne a lokacin wani ziyarar neman rahoto na musamman da wakilin mu a jihar ta Nasarawa ya kai hedikwatar su dake birnin Lafiya fadar gwamnatin jihar ranar Laraba na mako da ake ciki inda ya gana da su ɗaya bayan ɗaya game da yanayin sabbin tsare-tsare da salon jagorancin sabon shugaban nasu Abdullahi Bala da harkokin jin daɗin su inda suka tabbatar cewa tabbas suna samun kulawa da kauna dama horo na musamman gun janar manajan cikin shekara 1 kaɗai da ya yi akan kujera ta zama na musamman da yake yi da su akai-akai tun zuwan sa hukumar.

Sun ce a yanzu kuma akwai ingantattun dangantaka dake tsakanin su da sauran hukumomin tsaro dabandaban a jihar sabanin yadda lamarin yake a da inda a wasu lokutan ma acewar su sukan gudanar da ayukan sintiri tare na haɗin gwiwa kuma sabon shugaban nasu Abdullahi Bala ɗin ne yake tabbatar da hakan.

Jami’an tsaron NAYES ɗin na jihar Nasarawa wadanda aka gana da sun sun kuma yi amfani da damar inda suka yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da zabin da suka bayyana nagari wato na nadin janar manajan Abdullahi Bala a muƙamin inda suka ce tabbas gwamnan bai yi zabin duhun dare ba. 

Dangane da ire-iren ayyukan tsaro da hukumar tsaron nasu na NAYES ke gudanar a jihar sai jami’an tsaron suka bayyana cewa ayukan nasu sun hada da gudanar da sintiri na musamman a lungu-lungu da saƙo-saƙon jihar tare da tallafawa wajen rage cunkoso da gudanar da sintirin haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro a jihar kamar su ‘yan sanda da ‘yan jami’an tsaron farin kaya da sojoji da sauran su ba kawai a birnin ta Lafiya ba harda sauran garuruwa dake kewayenta baki daya kana suka kuma yi kira ga al’ummar jihar baki daya musamman matasa su guje aikata laifuffuka su zauna lafiya da junan su don duk wanda suka kama yana taka doka hukumar zata hukunta shi yadda yadace. 

Ita dai hukumar tsaron na musamman na gwamnatin jihar Nasarawa da ake kira NAYES din tsohon gwamnan jihar Umaru Tanko Al’makura ne ya kafa a lokacin mulkin sa inda tun daga lokacin ne ake ta kwashe dinbin matasan jihar ciki da nufin samar musu da aikin yi na musamman da kuma tallafawa bangaren tsaron jihar baki daya don yaki da rashin da’a da aikata laifuffuka da sauran ayyukan ta’asa a fadin jihar baki faya inda shi kuma sabon janar manajan hukumar na yanzu Abdullahi Bala gwamnan jihar mai ci yanzu Injiniya Abdullahi Sule ya nada shi muƙamin a bara shekarar 2024 da ya gabata.

By ukarofi