Dubban ƴan ƙasar Burkina Faso sun taru a Ouagadougou da wasu biranen ƙasar domin gudanar da gamgamin nuna goyon baya ga shugaban mulkin sojin ƙasar Kaftin Ibrahim Trawore, bayan wani gagarumin yunƙurin juyin mulki da gwamnatin ƙasar ta ce an yi.
Masu gangami da suka taru a tsakiyar babban birnin ƙasar Ouagadougou ɗauke da manyan – manyan alluna mai ɗauke hoton shugaban mulkin sojin ƙasar Kaftin Traore sun kuma ɗage tutocin Burkina Faso da na Rasha.
Har ila yau, suna rike alluna masu ɗauke da saƙonnin jinjina ga shugaban mulkin sojin da kuma ɗaukacin al’ummar Burkina Faso.
A ranar 21 ga watan Afrilun da ya gabata ne dai gwamnatin mulkin sojan ƙasar da ke yammacin Afirka ta yi ikirarin murkushe wani gagarumin juyin mulki da wasu mahara suka shirya daga makwabciyar ƙasar Cote d’Iɓoire, tare da kame wasu manyan hafsoshin sojojin ƙasar da ake zargi da hannu.
Traore, wanda ya ƙarbi mulki a wani juyin mulki da ya yi a watan Satumbar shekarar 2022, ya sha zargin Iɓory Coast da bai wa ƴan ta’adda mafaka don wargaza ƙasar da ke yankin Sahel, zargin da makwabciyarta ta ki amincewa da shi.
Gamayyar ƙungiyoyin Fararen hula ta CNAɓC masu goyon bayan gwamnatin soji ta kira zanga-zangar, wanda kakakinta ke cewa hakan wani mataki ne da tabbatar da jaruntar shugaban ƙasar.
“Mu al’ummomin da ke son adalci da ‘yancin kai, muna tabbatar da haɗin kanmu mara karewa ga jarumta da gwagwarmayar ƴan ƙasar Burkina Faso domin kwato musu ‘yancin kai.”
Kamar makwabtan Nijar da Mali, Burkina Faso ƙarƙashin Traore ta kau da kai daga Faransa da ta yi mata mulkin mallaka tare kuma da kulla alaƙa da ƙasar Rasha.
Dukkan ƙasashen uku na Sahel sun shafe gomman shekaru suna fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da masu ikirarin jihadi da ke da alaƙa da Al-ƙaeda da ƙungiyar IS.
ƙasashe uku ƙarƙashin jagorancin mulkin soja sun fice daga ƙungiyar ECOWAS a farkon wannan shekara, suna masu zargin ƙungiyar ƙasashen yankin da yin biyayya ga Faransa, inda suka kafa ƙungiyar kawancen ƙasashen Sahel (AES). RFI
