Taron tattauna makomar ƙasar wanda ya gudana tsawon makwanni ya buƙaci ayyana Janar Assimi Goïta a matsayin Shugaban Jamhuriya tare da ba shi damar cigaba da shugabancin ƙasar har na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Wakilai 137 daga cikin 297 da aka gayyata sun bada shawarar rusa illahirin jami’iyyun siyasa ƙasar da kuma yi wa tsarin riƙon ƙwarya kwaskwarima.
Haka ma, wakilan sun buƙaci a jingine duk wani batun da ya shafi siyasa har sai an samu ɗaurewar zaman lafiya a ƙasar.
A makon da ya gabata jam’iyyun siyasa da dama a ƙasar ta Mali suka yi zargin cewa gwamnatin mulkin sojin ƙasar na wani yunƙuri na ganin ta rusa su don kawo ƙarshen matsin lambar da take fuskanta daga masu fafutar ganin an dawo da dimokuraɗiyya ƙasar.
A watan Maris ɗin da ya gabata takwaransa na Jamhuriya Nijar Janar Abdurahmane ya rattaba hannu kan ƙudurorin doka da dama, da suka haɗa da rusa illahirin jam’iyyun siyasar ƙasar sama da 170 da kuma sallamar fursunonin da siyasa da ke tsare jim kaɗan bayan rantsar dashi a matsayin shugaban jamhuriya kamar yadda taron tattauna makoma ƙasar ya buƙata.
