
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Alhamis ne Hukumar Samar da Katin ɗan ƙasa, NIMC ta sauya tsarin farashin gudanarwarta bayan shekaru goma, lamarin da ya shafi kuɗin rajistar samun lambar ɗan ƙasa, wato NIN.
Babban jami’in hulɗa da jama’arta, Dakta Kayode Adejoke ya bayyana hakan a wata takarda, inda ya ce an yi sauyin ne don ya dace da farashin gudanarwa na wannan zamanin.
Haka kuma, hukuncin zai taimaka wajen samar da kati mai nagarta ga ƴan ƙasa da tabbatar da farashi mai sauƙi a gare su.
Dakta Adejoke ya ƙara da cewa, za a fara aiki da sabon farashin ne a nan take, ya na mai gargaɗi ga masu aikin rajistar da su kiyaye bin sabon tsarin tare da kauce wa karɓar farashin da ya wuce wanda ta amince da shi.
Ya kuma ce, za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a saɓa wa sabon tsarin, kamar yadda doka ta tanadar.
Kazalika, ya ce za su yi ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da adalci a yayin aiwatar da tsarin don ganin sun gamsar da al’umma.
Har’ilayau, ya ce za a wallafa sababbin tsare-tsaren kowane ɗaya daga cikinsu a shafin hukumar kamar haka; www.nimc.gov.ng ta yadda ƴan Nijeriya da sauran masu-ruwa-da-tsaki za su gani domin kiyayewa.
