
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Alhamis ne ƴan bindiga suka farmaki gidan tsohon Ciyaman ɗin Ƙaramar Hukumar Jama’are, Hon. Isah Muhammad a Jihar Bauchi, inda da kashe shi a unguwar Fadaman Mada dake garin Bauchi.
Wata majiya ta ce, maharan sun je gidan tsohon shugaban ƙaramar hukumar ne, wanda aka sani da Ɗan Galadiman Jama’are, inda suka rufe gidan sannan suka kashe shi a ciki.
Haka kuma, an raunata ƴaƴansa biyu a yayin aukuwar lamarin, waɗanda a yanzu suna wani asibiti a Bauchi domin karɓar magani, kamar yadda WikkiTimes ta ruwaito daga Zamani TV.
Marigayin ya kasance ɗaya ne daga cikin masu sarautar gargajiya da ake girmama su a Jama’are.
Zuwa lokacin kammala rahoton, ba samu wani jawabi daga rundunar ƴan sanda ko kama wani ba da hannu a ta’addancin ba.
