Natasha ta yi min tayin miliyan N200 don yi wa Akpabio ƙazafin safarar gaɓoɓin mutune – Sandra Duru

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Wata mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam da ke zaune a Amurka, Dr. Sandra Duru, ta bayyana cewa ta miƙa hujjojin tattaunawar waya tsakaninta da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda aka dakatar, ga hukumomin tsaro na cikin Amurka da sauran ƙasashe don gudanar da bincike ta hanyar gwajin fasaha. A wani faifan bidiyo da ta watsa kai tsaye a Facebook, Duru ta nuna shaidar kiran waya da saƙonnin WhatsApp da ke nuna cewa Natasha ta taɓa magana da ita, saɓanin ikirarin da ta yi a baya cewa ba ta taɓa saninta ba.

Dr. Duru, wadda aka fi sani da Prof. Mgbeke, ta ce Natasha ta ba ta tayin Naira miliyan 200 domin ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da safarar gaɓoɓin jiki da kuma da hannu a mutuwar wata yarinya mai suna Umoren da ta rasu a shekarar 2021. Ta ce Natasha ta ɗauki wannan mataki ne bayan ta kasa samun sakamako daga zargin cin zarafin da ta ɗora wa Akpabio. Duru ta buƙaci rundunar ƴan sandan Najeriya da hukumar Inter-Parliamentary Union (IPU) da sauran hukumomi na duniya su gudanar da bincike mai zurfi kan zarge-zargen da Natasha ke yi da kuma abinda ta sani game da mutuwar Umoren.

A cewarta, Natasha ta bayyana cewa babu wata hujja da ke nuna cewa shugaban Majalisar Dattawa ya ci zarafinta ko ya shiga harkar safarar gaɓoɓin jiki. Duru ta ƙara da cewa Natasha tana da mugun nufi na lalata mutuncin shugabanni maza da kuma jefa Najeriya cikin ruɗani. Ta ce Natasha na ikirarin cewa gwamnatin Yarbawa ce ake ƙoƙarin kifarwa, kuma tana da buri na zama gwamnan Jihar Kogi ko ministar albarkatun man fetur idan ta cimma nasarar kawar da shugaban majalisar.

By ukarofi