Seyi Tinubu ya musanta tayin cin-hanci, garkuwa da sa a doki Shugaban NANS

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ɗan Shugaba Bola Tinubu, wato Seyi Tinubu, ya ƙaryata zargin da Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya (NANS), Kwamared Atiku Abubakar Isah ya yi akansa, inda ya ce an yi haka ne da nufin ɓata masa suna.

Seyi Tinubu ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa ta kafar Instagram inda cikin mamaki ya ce bai taɓa tattauna wani batu da shi ba a Legas ko ko’ina a duniya.

Ya kuma ce, bai taɓa haɗuwa da shi ba, kamar yadda bai taɓa zuwa wani waje da ƴan daba ba.

Ya ƙara da cewa, baki ɗaya zarge-zargen da Kwamared Isah ya yi akan nasa ƙirƙirar su aka yi.

Hakan ya biyo bayan wani taron manema labarai ne da ya gudana a ranar Laraba, inda Shugaban na NANS ya yi ikirarin cewa Seyi Tinubu da Ministan Ci-gaban Matasa, Ayodele Olawande sun masa tayin cin-hancin Naira miliyan 100 don ya tallata Shugaba Bola Tinubu, amma ya ƙi amincewa.

Ya ce, ya yi hakan ne saboda ba zai iya tallata mutumin da ya gaza samar da sakamakon da aka zaɓe shi a kai ba.

Bayan haka ne ya ce, aka kitsa yadda za a yi garkuwa da shi, wanda a ranar 15 ga watan Afrilu ne aka samu nasarar yin hakan, sannan aka masa duka tare da sanya shi yin tsirara.

Ya kuma ce, akwai wasu da suka yi wa rayuwarsa barazana matuƙar ya bayyana abinda ya faru.

By Babaji