Tawagar farfaɗo da tafiyar Kwankwasiyya a Jihar Filato ta isa Wase

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

A wani ɓangare na cigaba da ƙoƙarin da jigo a cikin tafiyar Kwankwasiyya a Jihar Filato, Hon. Muhammad Shafi’u Yakubu Sahlan yake yi na ganin an ƙara tayar da tsimin masoya da magoya bayan madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da jam’iyyar NNPP da nufin farfaɗo da harkokin siyasar Kwankwasiyya a kowanne lungu na jihar, tsohon ɗan takarar Sanata a shiyyar Filato ta Arewa, ya ziyarci Ƙaramar hukumar Wase, domin ganawa da ‘ya’yan ƙungiyar da ke can.

A ranar Alhamis da ta gabata ne tawagar Kwankwasiyya Sahlaniyya ƙarƙashin jagorancin Hon. Shafi’u Sahlan ta shiga garin Wase, inda jagoran tafiyar ya yi zama na musamman da shugabannin Kwankwasiyya na yankin a ƙarƙashin jagorancin shugaban shiyyar Filato ta Kudu, Malam Abubakar Galadima.

Tattaunawar tasu ta mayar da hankali ne game da muhimman batutuwan da suka shafi sabon tsarin da aka fitar na yi wa tafiyar Kwankwasiyya garambawul a dukkan faɗin Jihar Filato bisa haɗin kai, da kuma tabbatar da goyon baya ga jagoran Kwankwasiyya na ƙasa Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso. Yayin da kuma aka ƙaddamar da sabon gangamin “I Concur With Kwankwaso For A Better Nigeria” wato #ICK4Better9ja2027.

Shugabannin sun bayyana farin cikinsu da wannan sabon tsari da suka ce ya zo a daidai lokacin da ya dace, tare da gabatar da jawabai na goyon bayan wannan tafiya ɗari bisa ɗari.

Shiyyar Kudancin Jihar Filato ya haɗa da ƙananan hukumomin Wase, Langtang ta Arewa, Langtang ta Kudu, Mikang, Shendam da Qua’an-Pan.

By ukarofi