Bauchi: Ana zargin abokan ɗan tsohon ciyaman da hannu a kashe shi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon Ciyaman na Ƙaramar Hukumar Jama’are dake Jihar Bauchi, Isa Muhammad Wabi ya rasa ransa a lokacin da wasu ƴan bindiga suka farmake shi a gidansa, inda ake zargin abokan ɗaya daga cikin ƴaƴansa, wato, Abdulgaffar mai shekaru 24 da hannu a kisan.

Rundunar ƴan sandan jihar, sun tabbatar da aukuwar lamarin a yayin da suka samu labarin harin da wasu matasa suka kai a unguwar Fadaman Mada a garin Bauchi, kamar yadda Kakakinta, CSP Ahmed Wakil ya bayyana a wata takarda.

Ya ce, sun samu tsohon Ciyaman ɗin, mai shekaru 66 a mawuyacin hali sakamakon raunukan da ya samu a yayin harin.

Daga nan ne aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Tafawa Ɓalewa don ba shi kulawar gaggawa, kana daga bisani ya rasu.

Bincike ya nuna cewa, wani mai suna Ahmad Abdulƙadir da aka sani da Abba da Farouk Malami da ake kira da Ajebo ne suka shiga gidan bayan kitsa yadda zasu kashe Wabi, inda suka yi nasarar daddaɓa masa wuƙa.

Haka kuma an ga Ajebo a yanayi na jikkata da ke nuna alamar an fafata da shi gabannin fitowarsa daga gidan.

Tuni aka tafi da Abdulgaffar wajen hukuma don yi masa tambayoyi da za su taimaka wajen samun bayanai akan lamarin da nufin gano baki ɗaya masu hannu a lamarin da hukunta su.

By Babaji