
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Jihar Bauchi da al’ummarta sun koka game da kisan tsohon shugaban Ƙaramar Hukumar Jama’are, Alhaji Isa Muhammad Wabi.
Binciken ƴan sanda ya nuna cewa, wasu abokan ɗansa ne suka farmake shi ne a gidansa dake unguwar Fadaman Mada a garin Bauchi.
A wata takarda da Mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Giɗaɗo ya fitar, Gwamna Bala Muhammad ya jajenta wa iyalan mamacin da al’ummar Masarautar Jama’are da sauran waɗanda alkhairansa suka kai gare su.
Ya kuma bayyana kaɗuwarsa game da aukuwar lamarin tare da umartar hukumar ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai mai zurfi gami da kamo baki ɗaya waɗanda aka samu da hannu a laifin da gurfanar da su domin su fuskanci hukuncin doka.
Gwamnan ya kuma yi kira ga iyaye a jihar da su ƙara kula da tarbiyyar ƴaƴansu gami da ababen da za su inganta su, wanda hakan zai taimaka wajen kare aukuwar irin haka a nan gaba.
Ya kuma yi addu’ar fatan samun rahamar Allah ga mamacin da bai wa makusantansa haƙurin juriya.
