Gwamnatin Tarayya ta bada wa’adi ga ƴan ƙasar waje da bizarsu ta ƙare

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwmantin Nijeriya ta bai wa ƴan ƙasar waje da bizarsu ta ƙare wa’adin watanni uku su fice daga ƙasar.

Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Shige-da-Fice (NIS), Akinsola Akinlabi ta faɗi hakan a wata takarda, ranar Juma’a.

Hukumar ta gargaɗe su da cewa, duk wanda aka samu da laifin zama sama da wa’adin da aka ba su, zai biya tarar Dala 15 da haramta sake shiga na tsawon shekaru biyar ko kuma na dindindin, hukuncin da zai fara aiki a watan Satumban 2025.

Sannan, wa’adin zai ƙare ne a ƙarshen watan Agusta.

Haka kuma takardar ta sanar da gabatar da tsarin tikitin shiga na yanar gizo ga ƴan ƙasar waje da na fita ga matafiya daga waje ta adireshi kamar haka__https://lecard.immigration.gov.ng.

By Babaji