FUDMA: Farfesa Raɗɗa ya kai ƙorafin Ministan Ilimi bisa zargin son kai a ɗaukar sabon VC

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

Wanda ke kan gaba wajen neman muƙamin mataimakin shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsinma (VC) dake Jihar Katsina, Farfesa Sadiq Raɗɗa, ya shigar da ƙorafi akan Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa bisa zargin sa da ƙoƙarin kitsa yadda za a cire sunansa daga cikin masu neman kujerar.

Raɗɗa, wanda Farfesa ne a Tsangayar Nazarin Zamantakewa ta Jami’ar Bayero dake Kano, ya ce duk da cewa ya cike dukkanin ƙa’idodin da ake buƙata, amma an soke da dama daga cikinsu ba tare da wasu ƙwararan dalillai ba.

Ya zargi VC mai barin gado, wato Farfesa Armaya’u Bichi da ƙoƙarin ƙaƙaba ɗan takarar da ke ƙasa da shi wajen cancanta.

A takardar ƙorafin nasa da ya aika wa ƙaramar Ministar Ilimi, Suwaiba Ahmad kuma Shugabar majalisar gudanarwa ta ASUU reshen FUDMA, ya ce Farfesa Bichi na ƙoƙarin kawo wani Farfesa Jamilu Shehu ne a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Ya ce, VC’n ya yi hakan ne da nufin yin rufa-rufa ga zargin badaƙalar kuɗaɗe da ɗaukar aiki da aka yi a Jami’ar, wanda ake fargabar a fallasa su.

Ya roƙi ministar da ta shiga tsakani tare da tabbatar yin adalci game da ƙorafin nasa ta yadda kowa zai samu dama irin yadda aka bai wa waninsa.

By Babaji